Jawabin Ghaddafi ya fusata mutane a Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Jawabinda shugaban kasar Libya Colonel Gaddafi, yayi a jiya cikin fushi ya gamu da adawar alummar yankin gabashin kasar wadanda suke adawa da shi.

Mutuminda ake gani a matsayin na biyun kanar Gaddafi wato ministan kula da harkokin cikin gidan kasar Abdel Fatah Yunes, ya bi sahun jerin manyan jam'ian dake adawa da shi.

Wakilin BBC ya ce 'yan kasar Libya dake gabashin kasar, sun maida martani cikin fushi da kuma fargaba, ga jawabin kanar Gaddafi na nuna jajircewa.

Fargabarsu ita ce, ba zai bar mulki ba sai ya ragargaza kasar.