Gaddafi na neman tabbatar da ikonsa

Kanar Gaddafi Hakkin mallakar hoto EPA

Shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi, na ci gaba da gwagwarmayar rike iko a yammacin kasar, ciki har da Tripoli babban birnin kasar.

Hakan na faruwa ne a yayin da masu zanga zangar adawa da shi wadanda ke samun goyon bayan wasu dakarun gwamnati da suka fandarewa gwamnati , ke kara karfi a gabashin kasar.

Mazauna birnin Tripoli sun ce, su na matukar fargabar fitowa, saboda tsoron dakarun Kanar Gaddafi za su bindige su da zarar sun gansu.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, yayi kira ga tarayyar Turai da ta dakatar da duk wata alakar tattalin arziki tare da kasar Libya, saboda tashin hankalin dake faruwa a kasar inda yace ana amfani da karfin da ya wuce kima wurin murkushe masu zanga zangar.

Rahotanni sun ce wasu 'yan kasashen waje dake Libyar na barin kasar, sakamakon wannan hargitsi.