Majalisar Dinkin Duniya ta la'anci gwamnatin Libya

Banki Moon
Image caption Taron kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin kasar Libya ke dauka na yin amfani da karfi akan farar hula.

Kwamitin sulhun ya kuma ce, tilas ne a dauki kwakkwaran mataki a kan duk wadanda ke da hannu a al'amarin.

A sanarwar bayan wani taron gaggawa da kwamitin ya yi a birnin New York, majalisar ta dinkin duniya ta kuma yi kiran a dakatar da tashin hankalin da ake yi a kasar ta Libya, kana kuma hukumomin kasar su biya wa 'yan kasar bukatunsu.

Sai dai kuma kwamitin bai dauki wani mataki ba a game da bukatar da jakadan kasar Libya ya nema na a sanya takunkumin hana shawagin jiragen sama a sararin samaniyar kasar don kare masu zanga zangar kin jinin gwamnati.