Daliban jami'ar Maiduguri na fargabar kora

Image caption Daliban makarantar sakandare a Najeriya

A Najeriya, wasu daliban jami'ar Maiduguri da dama na cikin fargabar fuskantar sallama daga makarantar sakamakon matakin da hukumomin jami'ar suka kudiri aniyar dauka kan duk wani dalibin da bai je ya gyara takardun sa ba na kammala karatun sakandire, musamman ma a bangaren Lissafi da Turanci.

Wasu daliban da lamarin zai shafa dai sun zargi hukumomin jami'r da neman take musu damar su ta kammala karatunsu a jami'a.

Sai dai hukumomin jami'ar sun musanta zargin inda suka ce wannan wata hanya ce ta kokarin kawo gyara a harkokin karatun daliban jami'o'in kasar da galibi suka dauko hanyar tabarbarewa.

An dai kiyasta cewa kimanin dalibai dake karatu a jami'ar dubu biyu ne wannan lamari zai shafa.