Hana yin zabe a wasu jahohin Najeriya

A Nigeria jama'a sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke a yau.

Kotun ta ce Hukumar zaben kasar ba ta da hurumin gudanar da zaben gwamnoni a wasu jihohin kasar biyar, a watan Aprilu mai zuwa.

Kotun ta ce wajibi ne a kyale gwamnoni Jihohin Sokoto da Adamawa da Kogi da Bayelsa da kuma Cross Rivers, su kammala wa'adinsu na shekaru hur-hudu, kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanadar.

Wadannan jiohohi na daga cikin jihohin da aka sake gudanar da zabe a cikinsu, bayan da kotun sauraren kararrakin zabe ta soke zabukan da aka yi a jihohin a watan aprilu na shekara ta 2007.