An jikkata masu zanga-zanga a Yemen

masu zanga zanga a kasar Yemen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An kashe mutum guda daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Ali Abdallah Saleh a kasar Yemen

Rahotanni daga kasar Yemen na cewa, an kashe mutum guda daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnati, kana aka jikkata wasu mutanen da dama a wani fito na fito da aka yi tsakanin masu adawa da kuma masu nuna goyon baya ga shugaba Ali Abdallah Saleh.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce, masu goyon bayan shugaban kasar dake dauke da makamai sun bude wuta akan masu zanga-zanga da suka taru a jami'ar Sana'a.

Tun daga watan Janairu ne dai aka soma samun tashin hankali a kasar ta Yemen, inda masu zanga-zanga ke neman, lallai shugaban kasar ya yi murabus.