Hukumar EFCC na binciken FAAN

Hukumar EFCC

Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta fara binciken wasu manyan jami'an hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya - FAAN.

Hukumar ta ce binciken ya shafi wasu korafe-korafe ne da kamfanin ya shigar da kansa da kuma wanda kamfanin Aevis da ke karbar haraji a madadin kamfanin FAAN, shi ma ya shigar.

Akwai zargin wasu kudade da suka tasamma Naira biliyan 25 sun salwanta.

Yanzu haka dai hukumar ta FAAN da kuma kamfanin Aevis da aka dorawa nauyin karbar haraji a tashoshin jiragen saman Lagos da Abuja, na zargin juna a kan bacewar kudin.