Shugaban Libya ya zargi kungiyar Alka'ida

Kanar Muammar Gaddafi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Har yanzu kura ba ta kwanta ba

Shugaban Libya, Mu'ammar Gaddafi, ya gabatar da jawabi ga jama'ar kasarsa a wani gidan talibin na gwamnatin kasar, a wannan lokaci da ake yin boren da ya yi sanadiyyar sa shi rasa iko a wasu sassa dake kasar.

Kanar Gaddafi dai ya gabatar da jawabinsa ne ba tare da an nuna hotonsa ba, kuma ya dora laifi kan Osama bin Laden, jagoran kungiyar Aqaeda kan tashin hankalin a ake fuskanta.

Ya kuma kwatanta abinda ke faruwa a matsayin ta'adanci daga kasashen waje.

Ya zargi wasu da ba a san ko su wane ne ba da sama wa matasan kasar kwayoyi da kuma giya.

Ya ce a bayyane take cewa 'ya,yan mu maza na yi wa kungiyar Alqaeda, ta Bin Laden aiki mutumin da kasashen duniya suka kira dan ta'ada.

Amurka da Tarayyar Turai da kuma sauran kasashen duniya na tare da mu a yakin da muke yi da su.