Obama yayi Allah-wadai da rikicin Libya

Shugaba Barrack Obama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Amurka Barrack Obama yayi Allah-wadai da zubar jinin da ake yi a kasar Libya.

A jawabinsa na farko tun bayan tashin hankalin da ya barke a Libya, shugaban Amurka Barrack Obama yayi Allah-wadai da zubar jinin da ake yi a kasar.

Mr. Obama ya ce, irin karfin da hukumomin kasar Libyan ke amfani da shi abin takaici ne, inda ya ce, gwamnatinsa zata duba irin matakan da zata iya dauka dangane da lamarin.

Amurka tana iya daukar matakin sanyawa Libya takunkumi, da kuma hana gwamnatin Libya taba kadarorinta.

Sai dai kuma wadannan matakai ba zasu taimaka ba nan take wajen kawo karshen tashin hankalin dake abkuwa a kasar.