Mazauna Abidjan na ci gaba da tserewa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mazauna Abidjan na ci gaba da tserewa

Daruruwan mazauna birni mafi girma a Ivory Coast wato Abidjan na ci gaba da tserewa fadan da ya barke tsakanin magoya bayan bangarori biyu dake takadddama akan shugabancin kasar.

Har ya zuwa tsakar daren alhamis an yi ta jin harbin bindigogi daga unguwar Abobo dake birnin na Abidjan.

Masu adawa da Laurent Gbagbo sun ce, sun kashe 'yan sanda da dama cikin makon nan.

Koda a ranar Litinin ma dai magoya bayan Laurent Gbagbo sun harbe magoyan bayan Alasan Ouattara akalla su shida.