Amurka ta sanyawa Libya takunkumi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Amurka Barrack Obama

Amurka ta sanyawa kasar Libya takunkumi, yayin da ita kuma majalisar dinkin duniya ke duba yiwuwar daukar mataki akan zubar da jinin da ake yi a Libyan.

Shugaba Obama na Amurka ya ce, gwamnatin Mua'ammar Gaddafi ta keta dokokin kasa da kasa na mutunta bil'adama.

Mr. Obama ya kuma sanya takunkumin hana kanar Gaddafi da iyalansa, da kuma manya jami'an gwamnatinsa taba dukiyoyinsu.

Wadannan matakai dai ba zasu kawo cikas ba ga yunkurin ceto rayukar jama'a, illa dai ana fatan zasu karfafa guiwar wasu dake goyon bayan kanar Gaddafi su bijire masa.