Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Wata uku na karshe

A lokacin da ciki ya shiga watanni uku na karshe wato tafiya ta dauko gangara. Wannan wani muhimmin lokaci ne a goyon ciki.

Domin a wannan lokacin ne wasu matan masu juna biyu dake da matsaloli na rashin lafiya kamar hawan jini da sauransu ke tashi.

Kuma wannan cuta ta hawan jini na daga cikin jerin dalilan dake janyo mutuwar kusan mace dubu daya a kowace rana a shekarar 2008 kamar yadda alkaluma suka nuna.

A wani nazari da kan dalilan dake haddasa mutuwar mata masu juna biyun a duniya, hukumar lafiya ta duniya WHO tace zubar da jini mai yawan gaske ne babban dalilin dake sanadiyyar mutuwar mata masu ciki a nahiyar Afrika da Asiya wato kashi 30 cikin dari na mata masu juna biyun da suka mutu.

Nazarin da hukumar tayi a shekarar 2006 ya kuma bayyan cewa a yankin Latin America da Carribean kuwa matsalolin da suka danganci hawan jini ne babban sanadin mutuwar mata masu juna biyu a wadannan yankuna.

A wani rahoton da WHO da asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da asusun kula da al'umma tare da Bankin duniya suka wallafa a bara ya nuna cewa manyan abubuwan da ke janyo mutuwar mata masu juna biyu cikin kai tsaye sun hada da zubar da jini mai yawan gaske, kamuwa da wasu kwayoyin cuta, haihuwar da kan zo da gardama, da ciwon hawan jini da kuma wasu matsalolin da kan taso da suka danganci ciki.

Shirin mu kenan na wannan makon. Ayi sauraro lafiya.