An bada kwangilar kera jiragen yaki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption jirgin sama kirar Boeing

Kamfanin kera jiragen sama na Amurka, wato Boeing ya sha gaban tsaransa na kasashen Turai, ta hanyar samun kwangilar kera jiragen yaki mafi girma a tarihi.

An dai baiwa kamfanin kwangilar ce ta kusan dala biliyan talatin da biyar domin maye gurbin tsoffin jiragen saman yaki na Amurka da ake amfani dasu wajen bada mai a samaniya ga wasu jiragen yakin.

Wakilin BBC ya ce, baya girman wannan kwangila, wani abu dake jan hakali kuma shi ne irin cece-kucen da ake ta yi akanta.

Jiragen yakin da za'a maye gurbinsu dai sun zarta shekaru hamsin ana amfani da su.