Neman hukunta masu hannu a rikicin Pilato

Rikicin jihar Pilato

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dake birnin Hague ta fara sauraron koke- koken da wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama su ashirin da biyar daga Najeriya suka mika mata dangane da rikicin jihar Pilato dake arewacin kasar.

Su dai wadannan kungiyoyin na neman kotun ne ta dauki matakin hukunta duk masu hannu a rikicin da aka jima ana fuskanta a jihar.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adaman dai sun mikawa kotun ta duniya bayanai da shaidu akan kashe-kashen dake abkuwa a jihar ta Pilato.

A nata bangaren, gwamnatin jihar Pilaton ta ce tana jiran samu takardun koke- koken da kungiyoyin suka mikawa kotun kafin ta maida martani akai.