Barkewar zanga zanga a Tunisia

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Yan sandan kwantar da tarzoma a Tunisia sun yi amfani da hayaki me sa hawaye, domin tarwatsa daruruwan masu zanga zanga a tsakiyyar Tunis baban birnin kasar.

Masu zangar dai na bukatar ganin cewa Firaministan kasar Mohammad Ghanouchi ya ajiye mukaminsa saboda ya shafe tsawon shekaru yana rike da mukamin firaminista karkashin mulkin shugaba Zine El Abidine Ben Ali, wanda aka hambarar da gwamnatinsa..

Sai dai an kuma sami wasu maza tare da yansandan da suka rufe fuskokinsu, sanye da tufafin farar hula, masu rike da sanduna , inda suka rika bin masu zanga zangar domin su kore su daga titunan birnin.