INEC zata kalubalanci hukunci kan zabe

Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da wata kotu ta yanke dangane da karin wa'adin wasu gwamnoni jihohin kasar su biyar.

Ta ce hukucin da kotun ta yanke zai shafi wasu manufofinta, a kan haka za ta garzaya kotu domin ta daukaka kara.

A makon da ya gabata wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukuncin cewa wa'adin mulkin wasu gwamnonin jihohi da aka sake zabe, ba zai kare ba, sai shejkara ta 2012, bayan kukan da suka shigar a gabanta, suna kalubalantar matakin da hukumar zaben ta dauka, inda ta ce wa'adin mulkinsu zai zo karshe a watan Mayun bana.