Ana ci gaba da nuna damuwa kan Libya

Akin kwashe 'yan gudun hijira a Libya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kasashen duniya na nuna damuwa kan rikicin Libya

Ana ta kara nuna damuwa a halin da dubban 'yan gudun hijira suke ciki - galibinsu ma'aikata 'yan ci-rani, wadanda ke kwararawa zuwa Tunisia daga Libya.

Kamar mutum dubu hamsin ne suka ketara suka shiga Tunisiar, rabinsu 'yan Tunisia.

Yanzu babban abinda aka sanya gaba shi ne sama masu isasshen abinci da makwanci.

Da yake magana a kan iyakar Libya da Tunisa, kakakin Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Firas Kayar ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka ma Tunisia.

Nijeriya ta shiga sahun kasashen dake kwashe 'yan kasarsu daga birnin Tripoli.