Masana siyasa na ganin Gaddafi zai sauka

Hakkin mallakar hoto Getty

Masana harkar da ta shafi siyasar kasa da kasa, sun nuna tabbacin yiwuwar nan ba da jimawa ba, Shugaban Kasar Libya Mu'ammar Gaddafi zai bayar da kai bori ya hau.

Sun dai bayyana cewa akwai yiwuwar nan da mako guda, wani abu na iya faruwa da zai sauya akalar al'amura a Libya.

Wannan kuma ya saba da jawabin da Shugaba Gaddafi ya yi a wata hira da ya yi da wani gidan talabijin na kasar Serbia, inda ya ce takunkumin da Kwamitin Sulhu na majalisar dinkin duniya ya saka masa haramtacce ne.

Shugaba Gaddafi ya yi watsi da takunkumin da majalisar dinkin duniya ta saka masa na hana shi bulaguro zuwa wasu kasashen, da kuma hana shi taba kadarorinsa dake kasashen yammacin duniya.

Shugaba Gaddafi ya kuma ce wasu 'yan tsiraru ne kawai ke adawa da mulkinsa amma an yi musu kawanya kuma za'a murkushe su.

Wannan kuma na faruwa ne a yayin da masu zanga zanga ke kara fadada yankunan ikonsu a Libya.