Fulani sun kai karar Najeriya ECOWAS

A Najeriya, wata Kungiyar Makiyaya mai suna Miyetti Allah Kautal Hore ta shigar da karar Gwamnatin tarayya kasar a gaban kotun kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS CEDEAO.

Kungiyar Miyetti Allah dai na neman a biya diyyar sama da Naira Miliyon Dubu Dari Hudu da Tamanin ga magadan Fulani dari biyu da tara da suka rasa rayukansu a sanadiyyar tashin hankalin Jihar Filato.

Kungiyar ta kuma nemi da a biya diyya akan dukiyar Fulanin da aka lalata wadanda suka hada da gidaje da dabbobi.

Kungiyar dai ta zargi gwamnati ne da yin sakaci wajen shawo kan rikicin.