An kashe mutane biyar a kauyen Kuru da ke Jos

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga Jihar Filaton Nijeriya na cewa an kai wani hari a kauyen Kuru da kusa da Jos babban birnin Jihar inda kuma aka hallaka wasu mutane biyar dukkaninsu 'yan gida daya.

Rahotannin sun ce an kai harin ne a daren jiya inda aka ce wadanda suka kai harin sun yi amfani da bindigogi wajen kashe mutanen.

Hukumomi a Jihar sun ce tuni suka fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka akai wannan hari.

An dai dade ana fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa a jihar ta Filato dake tsakiyar Nijeriya inda mutane da dama suka rasa rayukansu.