Mataimakiyar Sakatariyar harkokin wajen Amurka na Najeriya

A Najeriya, mataimakiyar Sakatariyar harkokin wajen Amurka Maria Otero, ta fara wata ziyarar kwanaki uku a kasar.

Ana sa ran ziyararar ta ta za ta maida hankali wajen yadda za a bunkasa cibiyoyin dimokradiyya da hanyoyin shirya zabuka, da kuma rawar da Najeriya ke takawa a fannin tsaro da ayyukan samar da zaman lafiya a nahiyar Afrika.

Ziyarar ta ta na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage makwanni kadan kafin a gudanar da babban zabe a Najeriya.

A kwanakin baya ma wata babbar tawaga daga kungiyar kasahe renon Ingila wato Common Wealth ta yi irin wannan ziyarar.