MNSD Nasara za ta ci gaba da aikin da Tanja ya fara

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A jamhuriyar Nijar dan takaran Jam'iyar MNSD Nasara a zaben shugaban kasa zagaye na biyu Alhaji Seyni Umaru ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da ayyukan gina kasa da tsohon shugaban kasar Tanja Mamadu ya soma.

Dan takarar dai ya bayyana cewa ya sha wannan alwashi ne domin kyautata jin dadin rayuwar jama'a.

Alhaji Seyni Umaru ya samu goyon bayan kawancen ARN ne a zaben.

Kuma Jam'iyun da ke mara masa baya sun yi alkawalin tayar da magoya bayansu daga barci domin cimma nasara.