An dage haramci a kan En Nahda a Tunisia

Tutar Tunisia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jam'iyyun da aka haramta sun fara gani a kasa

Mahukuntan Tunisia sun halatta kungiyar masu kishin Islama ta Ennahda, wanda shi ne karan farko tun bayan da aka kafata shekaru talatin din da suka wuce.

Za a bar kungiyar Ennahda ta kafa jam'iyyar siyasa kuma ta shiga zabukan da za ai nan gaba a kasar.

Ba a dade ba da shugaban kungiyar ya koma gida bayan kwashe shekaru yana gudun hijira a waje.

Masu aiko da rahotanni sun ce kungiyoyin masu kishin Islama sun taka rawa a gwagwarmayar neman kafa demokradiyyar da ta keta kasashen Larabawa, sai dai kuma ba su ne aka gani a gaba gaba ba a gwagwarmayar.