An yanke wa mutane 11 hukuncin kisa kan harin Gujurat a India

Wata kotu a Jahar Gujurat ta Kasar India ta yanke hukuncin kisa akan wasu musulmai goma sha daya, bisa laifin cunna wa wani jirgin kasa wuta a garin Godhra shekaru taran da suka wuce.

Hakan dai ya jawo tashin hankali mafi muni da aka taba yi a India, tun bayan samun 'yancin kanta.

Haka nan kuma kotun ta yankewa wasu mutanen ashirin hukuncin daurin rai da rai, bisa rawar da suka taka a harin da aka kai a tashar jirgin kasa ta Godhra, wanda ya yai sanadiyyar rayukan mabiya addinin hidu 59.

Lamarin ya haddasa tashe tashen hankula, inda mutane fiye da dubu suka rasa rayukansu, yawancinsu Musulmi.