PDP da ACN sun yi yakin neman zabe a Legas

Jama'iyar PDP mai mulki a Najeriya ta gudanar da yakin neman zabenta na Shugaban kasa a Jihar Legas, jihar da take tamkar gagarau ga jama'iyar.

Tun dai lokacin da aka koma mulkin demokuradiya a Najeriya Jama'iyar ta PDP ta ke kokarin ganin ta kama jihar ta Legas, amma abun ya faskara.

A kwanan baya dai Shugaba Goodluck Jonathan ya ce, yankin kudu maso yammacin Nigeriar, yana da muhimmancin gaske ta yadda bai kamata a bar shi a hannun wadanda ya kira "Yan Iska" ba.

Yayinda kuma Shugaban kasar ke yakin neman zaben nasa a Legas ita ma Jama'iyar ta ACN tana gudanar da nata gangamin a wani yanki na birnin