PDP ta kalubalanci 'yan adawa akan Cif Olabode

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta mayar da martani a kan sukar da wasu Jam'iyyun adawa suka yi mata dangane da bikin da wasu suka yi don tarbar Cif Olabode George bayan sako shi daga kurkuku.

Shugaban Jam'iyyar PDP, Dr. Bello Halliru ya ce masoya Cif Olabode George suna da ikon nuna murnar su, amma ba wani lamari ne da za a danganta shi da PDP ba.

Mista Olabode George dai shine tsohon Shugaban Hukumar gudanarwar tashoshin jiragen ruwan Najeriya, kuma wani jigo a Jam'iyyar ta PDP.

A shekarar 2009 kotu ta same shi, shi da wasu mambobin hukumar da laifin cin hanci da rashawa.

A bangare guda kuma tsohon Manajan Daraktan hukumar Alhaji Aminu Dabo ya ce sun garzaya kotun koli dan kalubalantar samun su da laifi da wata kotun kasar ta yi a baya, wanda hakan ya janyo musu zaman gidan kaso na sama da shekara daya.

Alhaji Aminu Dabo wanda aka daure shi tare da tsohon Cif Olabode Goerge a ranar 25 ga watan Oktobar 2009, sun futo ne daga gidan kaso a ranar Juma'ar makon jiya.

Alhaji Aminu Dabo ya ce suna so ne a wankesu daga laifin da babbar kotun kasar ta tabbatar musu, in da ya ce lamarin na da dangantaka da siyasa.