'Lemon kwalba na janyo hawan jini' - In ji Likitoci

Hakkin mallakar hoto google

Shan lemon kwalba da aka tsuga wa sukari da yawa na kara hawan jini in ji likitoci.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa shan lemon gwangwani a kullum na kara yawan mizanin hawan jini.

Wani gwaji da aka yi a kan mutane 2,500 ya nuna cewa, shan lemon kwalba da kuma matsatsun ruwan 'ya-'yan itatuwa da ake sarrafawa da ya kai 355ml a kullum na kawo matsala ga lafiyar dan-adam.

An dai wallafa wannan bincike ne a mujallar ciwon suga da wasu masana a Burtaniya da Amurka su ka yi.

Gwajin ya kara nuna cewa lemon kwalban da ba su da zaki sosai basu da hatsari ga lafiya.

Gwajin Fitsari da Jini

A karo hudu dai, an yi gwaji akan wasu mutane da ke zaune a Burtaniya da Amurka da shekarunsu ke tsakanin 40-59, inda aka sanya su rubuta abin da suka ci a ranar kuma bayan kwana guda aka gwada fitsarinsu da kuma jinin su.

Hakkin mallakar hoto spl
Image caption Shan lemo mai su kari dayawa na janyo hawan jini

Masu binciken sun gano cewa an samu karin sukari a wadanda suke shan lemon kwalba mai zaki a kullum.

An kara gano cewa wadanda ke shan lemun kwalba da wadanda su ka danganci kayan zaki fiye da sau daya a rana, sun fi samun ciwon hawan jini fiye da wadanda ba sa shan abubuwan da suka danganci suga.

Gabaki daya dai mutanen da ke shan lemun kwalba mai zaki an gano cewa basu da koshin lafiya kuma suna da kibar da ta wuce kima.

Amma duk da haka, akwai hawan jini tattare da su.

Shanyewar bangaren jiki

Farfesa Paul Elliott, wani wallafi a sashen lafiya ta kwalejin Imperial da ke London ya ce; "A sane yake a baya cewa idan mutum na shan gishiri da yawa, akwai yiwuwar zai kamu da hawan jini."

"Wannan bincike da aka gudanar ya kara nuni da cewa shan sukari da yawa ma na iya haddasa hawan jini."

Hawan jini na iya haddasa bugawar zuciya kuma.

Wanda ke ma'aunin hawan jinin da ya kai 135mmHg da ya haura 85mmHg akwai yiwuwar zai iya samun bugun zuciya ko kuma shanyewar bangaren jiki.

A binciken da aka gudanar an lura cewa mutanen da su ka fi shan suga da kuma gishiri sun fi kamuwa da hawan jini.

Cibiyar kula da masu ciwon zuciya ta Burtaniya ta ce sai an kara bincike domin karin sannin yadda suga ke hadasa hawan jini.

Victoria Taylor, wata jami'a a cibiyar ta ce kamata ya yi mutane su guji shan abubuwan masu zaki domin gujewa hawan jini da kuma ciwon zuciya da kuma yin kibar da ba ta da kima.

Farfesa Graham MacGregor, Shugaban kungiyar masu ciwon hawan jini ya ce binciken ba zai yiwa masu siyar da lemon kwalba dadi ba.

"Lemon kwalba na kara kiba kuma yana sanya hawan jini... Dolene mu guje su gabaki daya."