An kama wani babban Malami a Sokoto

'Yan Sandan Nigeria
Image caption 'Yan Sandan Nigeria

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da na addini a Najeriya sun bayyana damuwarsu game da ci gaba da tsare wani fitaccen malamin addinin musulunci da gwamnati ke yi.

An kama Sheikh Abubakar Jibril Farfaru ne a Sokoto bisa zargin shafawa hoton Shugaba Goodluck Jonatan bakin Fenti.

Yan sanda ne dai suka kama limamin massallacin Jumu'a na Farfaru da ke birnin Sakkwato tare da wasu na kusa da shi su hudu bisa zargin kokarin tayar da rikici.

Kamar yadda rundunar yan sanda ta Jihar Sokoto ta ce, abun da limamin ya aikata laifi ne a tsarin dokokin Najeriya.

Kungiyar Kare Hakkin bil adama ta Civil Rights Congress tayi Allah wadai da kamen tana mai cewar matakin wani aiki ne na gwamnatin kama karya.