An harbe wani Minista a Pakistan

Image caption Shabaz Bhatti

'Yansanda a Pakistan sun ce wani dan bindigar da ba a san ko wanene ba ya harbe Ministan harkokin tsararru a kasar, Shahbaz Bhatti, har lahira.

Shi ne mutum na biyu a cikin jam'iyyar PPP mai mulki da aka kashe a cikin watanni.

Wannan kisa dai ya kara fitowa da yadda yanayin tsaro ke da rauni a Pakistan fili. Sufeto Janar na 'yan sandan kasar a Islamabad, Wajid Ali Durrani, ya ce Mista Bhatti na kan hanyarsa ne zuwa aiki lokacin da 'yan bindiga suka bude masa wuta.

"Lokacin da ya bar gidansa, sai wata farar mota dauke da 'yan bindiga uku zuwa hudu wadanda suka rufe fuskokinsu, ta tare shi, daga nan sai suka bude masa wuta.

Wadansu wadanda suka ganewa idanuwansu abin da ya faru kuma sun ce wadansu 'yan bindiga biyu ne suka tare motar Mista Bhatti suka harbe shi sannan suka tsere.

An dai yi amanna cewa dalilai na addini ne suka sa aka kashe Mista Bhatti.

'Yan sanda sun ce an samu wata takarda a inda aka kashe shi wadda ke zargin Mista Bhatti da yin batanci ga Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Ministan dai ya kasance yana kiran a soke dokar nan mai tsauri da haramta sabo a kasar.

A wani faifan bidiyo da wata kungiya ta ce ya dauka watanni hudu da suka gabata ya kuma bayar da wasiyyar cewa in ya mutu a mikawa gidajen talabijin na BBC da Aljazeera, Mista Bhatti ya ce ba ya shakkar sadaukar da ransa.

Mista Bhatti, wanda Kirista ne, ya goya baya ga Aasia Bibi, wata mata Kirista wadda aka yankewa hukuncin kisa saboda aikata sabo.

Wadansu mutane a Pakisatn din dai na ganin wannan da kuma yekuwar da ya ke yi ta soke dokar sabo, su ma aikata sabo ne.

A watan Janairun da ya gabata ma dai an bindige wani gwamnan lardi, Salman Taseer, bayan ya yi alkawarin zai sa shugaban kasar ya yiwa Asia Bibi ahuwa.