Kotu ta tabbatar wa Muhammad Abacha takara a Kano

Janar Muhammadu Buhari
Image caption Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar CPC, Janar Muhammadu Buhari

Wata babbar kotun tarayya da ke Abujan Najeriya, ta tabbatar da Muhammad Sani Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar CPC a jihar kano.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun mai shari'a Kolawole Gabriel, ya ce bisa ga hujjojin da aka gabatar masa, Muhammad Abacha shi ne ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar kuma, jam'iyar CPC ta saba doka da ta sauya sunansa a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano.

Alkalin kotun ya kuma umarci dan takarar da jam'iyar CPC ta mika sunansa ga hukumar zabe, Brigediya Lawal Jafaru Isa mai ritaya da ya daina bayyana kansa a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar.

Sai dai lauyan jam'iyar CPC Barrister Ahmed B. Mahmud ya ce jam'iyar za ta dubu yiwuwar daukaka kara kan hukuncin kotun.

A baya ma wata kotun tarayya da ke zamanta a Abujan, ta umarci hukumar zaben da kada ta amince da dan takarar da jam'iyyar ta CPC ta mika mata a zaben gwamna daga jihar Katsina.