Harin jirgin sama a birnin Brega da ke Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan adawa na kokarin harbo jiragen sama.

Sojojin saman Libya sun kai hari a filin saukar jiragen sama na garin Brega da ke gabashin kasar.

Wani kakakin 'yan adawa ya ce jiragen sama sun yi ruwan bama-bamai a filin saukar jiragen sama.

Ba a dai samu rahoton asarar rayuka ko kuma rauni ba a harin da jiragen suka kai.

'Yan adawa ne dai ke rike da iko a garin na Brega wanda ke da dimbin arzikin man fetur.

An kai harin ne bayan kwana guda da da sojojin da ke biyayya ga Kanal Gaddafi da kuma 'yan adawa suka fafata inda kuma mutane 14 suka mutu.

Sojojin da ke biyayya ga Gaddafi dai sun kwace garin daga bisani, kafin 'yan adawa su kora su.