Jam'iyyun adawa sun zargi PDP da hana musu kamfe

A Najeriya, wasu manyan jam`iyyun adawar kasar uku na zargin jam`iyyar PDP mai mukin kasar da amfani da iko wajen hana su amfani da wuraren taro na gwamnati musamman a wasu jihohin kasar.

Jam`iyyun dai sun ce ana hana `yan takararsu na shugaban kasa wuraren da za su gabatar da tarukan yakin neman zabe ko ma hana musu yin taron baki daya.

Jam`iyyun wadanda suka hada da CPC da ACN da kuma ANPP sun ce za su yi iya kokarinsu wajen ganin cewa jam`iyyar PDP ba ta yi nasarar taka musu birki ba.

Sai dai Jam`iyyar PDP ta musanta wannan zargi, ta ce aikin jami`an tsaro ne ke da ikon bari ko hana wani yin taro.

Jam`iyyun dai sun yi zargin cewa irin jama`ar da suke tarawa a wajen tarukansu na yakin neman zabe ne ke firgita jam`iyyar PDP, kuma wannan ne ya sa take kitsa makirci ta hanyar amfani da madafan iko kasancewar ita ke mulkin kasa wajen hana jam`iyyun adawa wurin taro na gwamnati, ko ma hana musu yin taron dungurungum.

Ita jam`iyyar CPC ta koka da irin halin da ta samu kanta a jihar Niger, inda ta yi zargin mahukunta sun hana mata dandalin baje-kolin jihar, matakin da a yanzu haka ya tilasta mata yin taron kaddamar da dantakarar shugaban kasarta, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, na shiyyar arewa-ta- tsakiya a filin Polo da ke Minna.

Babban abin da jam'iyyun adawa suka ce na daure musu kai dai shi ne yadda ita jam`iyyar PDP ba ta taba fuskantar irin wannan takurawar ba.

Masu lura da al`amura dai na ganin cewa irin wannan takun - saka tsakanin jam`iyya mai mulki da jam`iyyun adawa alama ce da ke nuna cewa har yanzu siyasar kasar ba ta kai wani matakin da za a ce al`adar juriya da hakurin mu`amala da juna sun shiga zukatan jam`iyyun siyasar kasar ta yadda a za a yi siyasa ba tare da gaba ba.