Bom ya fashe a Sulejan Najeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani bom ya fashe a wurin wani taron siyasa a agarin Suleja da ke jihar Niger dake makwaftaka da Abuja.

Fashewar ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane uku yayinda kimanin ashirin da daya suka samu raunuka.

Rahotanni sun nuna cewa an jefa bom din ne daga cikin wata mota da ke gudu a lokacin da take wuce taron siyasar, abinda ya sa bom din ya kaucewa taron ya fada kan jama'ar da ke kusa da wajen inda wata mata ke kasuwancinta.

Harin dai na zuwa ne wata guda kafin zabubbukan gama gari da za a gudanar a kasar.

I zuwa yanzu dai 'yan sanda ba su bayyana ko su wa ake zargi da kai harin ba.

Hare-Hare

Ana dai dada samun karuwar kai hare-haren bama-bamai a lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zabubbuka a kasar da ta fi kowacce fitar da danyen man fetur kasuwannin duniya daga nahiyar Afrika.

Harin bom dinda aka kai a ranar bikin murnar kasar cikar shekaru hamsin da samun 'yancin kai, da kuma wanda aka kai a jajiberen sabuwar shekara a Abuja da kuma wanda aka kai a jajiberen bikin Kirsimeti a garin Jos ya sanya jama'a da dama na tsoron irin abinda ka iya faruwa a lokacin zaben da za a yi nan gaba a kasar.

A watan Janairun da ya gabata wasu 'yan bindiga sun harbe dan takarar mukamin gwamna na jam'iyyar ANPP a jihar Borno da ke arewacin kasar.

An kuma kai wasu hare-haren da nakiyoyi a kan ofisoshin jam'iyyun adawa a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur da ke kudancin kasar.

A watan da ya gabata, tarayyar turai ta ce rikice-rikicen da ake fama da su a tsakiya da arewacin Najeriya, sun yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 300.