Kotu ta tabbatar wa Muhammad Abacha takara a Kano

Hakkin mallakar hoto city flavour
Image caption Mohammed Abacha

Wata babbar kotun tarayya da ke Abujan Najeriya, ta tabbatar da Muhammad Sani Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar CPC a jihar kano.

Da yake yanke hukunci alkalin kotun mai shari'a Kolawole gabriel, ya ce bisa ga hujjojin da aka gabatar masa, Muhammad Abacha shine ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyar kuma, jam'iyar CPC ta saba doka data sauya sunansa a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano.

Alkalin kotun ya kuma umurci dan takarar da jam'iyar CPC ta mika sunansa ga hukumar zabe, Brigediya Lawal Jafaru Isa mai ritaya da ya daina bayyana kansa a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar.

Sai dai lauyan jam'iyar CPC Barrister Ahmed B. Mahmud ya ce jam'iyar zata dubu yiwuwar daukaka karar hukuncin kotun.

A baya ma wata kotun tarayya da ke zamanta a Abujan, ta umarci hukumar zaben da kada ta amince da dan takarar da jam'iyyar ta CPC ta mika mata a zaben gwamna daga jihar Katsina.