Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Amfani da 'yan sanda wajen takurawa 'yan adawa

Image caption An dade ana zargin 'yan sandan Najeriya da marawa gwamnati baya

A Najeriya, yayin da zabe ke matsowa, ana ta kara samun tabarbarewar tsaro a sassa daban-daban na kasar.

Inda a wasu jihohin aka yi taho mu gama tsakanin bangarorin dake hamayya da juna a siyasance, yayin da a wasu johohin kuma jam'iyya mai mulki ce ke amfani da jam'ian tsaro wajen hana gangamin 'yan adawa.

Kuma wata sabuwar barazanar tsaron da ke kunno kai ita ce ta tashin bam a dandalin yakin neman zabe, abinda yasa wasu ke ganin cewar rundunar 'yan sandan kasar ba ta shirya ba wajen tabbatar da tsaro a lokacin zaben dake tafe.

Sai dai kuma a hirarsa da Aliyu Abdullahi Tanko, Speto janar na 'yan sandan Najeriya, Alhaji Hafiz Abubakar Ringim, ya karyata zarge-zargen rashin yiwa 'yan adawa adalci: