Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Haihuwar bakwaini

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A wani nazari da hukumar lafiya tayi a karo na farko a shekarar 2005 don kiyasta yawan bakwaini da ake haihuwa a duniya, ya bayyana cewa a kalla kashi kusan goma cikin dari na haihuwar da akayi a wannan shekarar bakwaini ne.

Wato daidai da haihuwa kusan miliyan goma sha uku cikin kusan haihuwa miliyan 115.3 da aka kiyasta an samu a duniya a shekarar.

Nazarin dai yayi kokarin fidda kiyasin bakwaini a fadin duniya, da kuma yadda ake samunsa a bangarori daban daban na duniya ya tattara bayanai daga kasashe 92 cikin kasashe 179 da akayi sharhin akansu.

Haka kuma a cewar nazari kashi 85 cikin dari na bakwainin da aka haifa a shekarar an same su ne a nahiyar Afrika da kuma Asiya, wato kusan haihuwa miliyan goma sha daya kenan.

Yayinda aka sami bakwaini dubu dari biyar a nahiyar Turai. haka alkaluman ma suke a arewacin America sai yankin Latin America da Carrebian da aka sami haihuwar bakwaini dubu dari tara a shekarar 2005.

Hukumar lafiyar ta duniyar dai ta kuma bayyana cewa haihuwar bakwaini kusam miliyan 13 da ka samu a shekarar ta 2005 ya kara asassa matsalar da ta riga ta dabaibaye fannoni kamar na lafiya, ilimi, samar da ababen more rayuwa a duniya.

Kodayake acewar nazarin hukumar babu wasu alkaluma da aka wallafa game da kididdgiar bakwainin da ake haihuwa a fadin duniya, amma daga alkaluman dake akwai sun nuna cewa an samu gagarumin karuwar haihuwar bakwaini a kasashen da suka ci gaba.

Wadannan kasashe sun hada da Amurka, Burtaniya da kasashen dake yankin Scandinavia an samu karuwar haihuwar bakwaini a cikin shekaru ashirin da suka gabata.

A shekarar ta 2005 an kiyasta cewa Amurka ta kashe kimanin sama da dala miliyan ashirin kan abubuwan da suka danganci kula da lafiyar bakwaini a kasar.

Asusun tallafawa yara ta majalisar dinkin duniya ya ce duk shekera jarirai bakwaini sama da miliyan daya ne ke mutuwa a fadin duniya.

A wani nazari na baya-bayan nan da hukumar lafiyar ta duniya ta yi domin duba sassan duniyar da matsalar haihuwar bakwaini ya fi kamari don sanin matakan dauka game da matsalar, hukumar tace daga bayanan da suka samu, anfi samun yawaitar haihuwar bakwaini a Afrika ne saboda watakila dalilan da suka hada da kamuwa da cututtuka da mata masu juna biyu kanyi ko kuma rashin isassun magunguna.

Shirin mu kenan na wannan makon, a yi sauraro lafiya.