Ya kamata a dauki matakan tsaro a Najeriya-Janar Babangida

Janar Ibrahim Babangida
Image caption Janar Ibrahim Babangida ya yi kira ga jama'a da su tashi tsaye

Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya maida martani ga harin bam din da ya auku a jiharsa, inda yace akwai bukatar karin matakan tsaro a kasar.

Hukumomi dai sun ce mutane uku ne su ka mutu a harin bom din da aka kai a garin Suleja na jihar Naija da ke makwaftaka da birnin tarayya Abuja.

Sai dai kafofin yada labarai a kasar na cewa kimanin mutane goma ne suka rasa rayukansu a harin.

Janar Babangida ya kuma ce, a irin halin da ake ciki kamata yayi mutane su rika lura da kuma sa ido dan kare kansu daga duk wata barazanar tsaro.

Ya ce idan da jama'a suna taimakawa jami'an tsaro, to da irin wadannan hare-haren ba su afku ba.

"Irin wadan nan abubuwa ba za su faru ba a kasashe irinsu Ingila, saboda suna da karfin gano duk wanda ke da hannu", kamar yadda ya shaida wa wakilin BBC Isa Sanusi.

Sai dai Babangida ya ki amince wa da batun da wasu ke yi na cewa hare-haren da ake yawan samu a kasar gazawa ce ta gwamnatin jam'iyyarsu ta PDP.