INEC ta yi rijistar mutane miliyan 73

Jega
Image caption Shugaban Hukumar zabe ta INEC Farfesa Attahiru Jega

A Najeriya Hukumar zabe mai kanta ta INEC, ta ce ta yiwa 'yan kasar miliyan 73, 528, 40 rijista domin kada kuri'a a zabukan da za a yi a watan Afrilu mai zuwa.

Wannan adadi ya zarta na wucin gadin da hukumar ta bayar a baya.

Hukumar ta kuma ce ta gano kimanin rijista dubu dari 870 wadanda aka yi ba bisa ka'ida ba.

Rijistar masu zaben dai wani muhimmin mataki ne a shirye-shiryen zaben da Hukumar ke yi.

Mukaddashin daraktan yada labarai na Hukumar zaben Mr Nick Dazen, ya shaida wa wakilin BBC Naziru Mika'il cewa sai da suka tantance duk wasu abubuwa ba su dace ba, sannan suka samu wannan adadin.

Ya kara da cewa alkaluman sun saba wa na baya ne, saboda dama sun bayyana cewa adadin da suka bayar a baya na wucin gadi ne.

Jihar Legas ce kan gaba a yawan masu kada kuri'a, inda take da mutane miliyan shida da doriya, sai jihar Kano mai mutane miliyan biyar da 'yan kai.

Yayin da jihar Naija wacce a baya aka ce tana da mutane dubu dari bakwai, a yanzu take da mutane miliyan biyu da doriya.

Dama dai kimanin 'yan kasar miliyan saba'in ne ake saran sun cancanci kada kuri'a a zaben mai zuwa.