An kama dan takarar gwamna na CPC a Katsina

Sanata Lado Danmarke
Image caption Sanata Lado Danmarke na da magoya bayan sosai a Katsina

A Najeriya rahotanni daga jihar Katsina sun ce 'yan sanda sun yi awan gaba da dan takarar gwamna na jam'iyyar adawa ta CPC a jihar, Sanata Yakubu Lado Danmarke.

A daren jiya ne dai 'yan sandan suka yi awangaba da Sanatan a wani Otel din da yake zaune a birnin Katsina.

Hakan daim ya zo ne a daidai lokacin da shi da magoya bayansa ke shirin gudanar da wani gangamin yakin neman zabe a garin Daura.

Wakilin BBC a Katsina Abba Muhammad, ya ce kamen nasa ba zaim rasa nasaba da tarzomar ta faru tsakanin magoya bayansa da kuma tawagar gwamnan jihar ba a makon da ya wuce.

Shima kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Katsina Ibrahim Abubakar, ya tabbatar wa BBC cewa Lado Danmarke na nan a hannunsu, inda suke masa tambayoyi.

Ya kara da cewa sun samu korafe-korafe game da yadda magoya bayansa suka nuna rashin da'a ga tawagar gwanma Ibrahim Shehu Shema na jihar ta Katsina.

Karin bayani