Tashin hankali na karuwa a biranen Libiya

Birnin Tripoli a yau Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Birnin Tripoli a yau

Dakaru masu biyaya ga jagoran Libiya, Kanar Gaddafi, suna fafatawa a fagen daga biyu, yayin da gwamnatin ke ta kokarin sake jaddada ikonta.

A daya daga cikin manyan biranen Libiyar, Zawiyah, mai nisan kilomita 50 a yamma da Tripoli babban birnin kasar, shaidu sun ce mutane dayawa sun hallaka, yayin da dakarun gwamnati ke kokarin sake kwace birnin na Zawiyah.

A gabashin Libiyar kuma, a kewayen garin Ras Lanuf mai tashar mai, sojojin gwamnati sun yi amfani da bindigogin atilare da jirage masu saukar angulu akan mayakan 'yan adawa.

Dakarun tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harsasan roba a birnin Tripoli bayan sallar Juma'a, domin tarwatsa daruruwan masu zanga zangar neman ganin bayan Kanar Gaddafi.

Hukumar 'yan sanda ta duniya, Interpol, ta yi kira ga kasashe da su sa ido sosai akan Kanar Gaddafi da danginsa da mukarrabansa su kimanin 15.