Ana ci gaba da artabu a Libya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu adawa da gwamnatin kanar Gaddafi a Libya

Ana ci gaba da artabu tsakanin 'yan tawaye da sojojin dake biyaya ga shugaban Libya Kanar Gaddafi wadanda ke neman karbe iko a garin Zawiyya dake kusa da birnin Tripoli, inda 'yan tawayen keda iko.

Jerin motocin yaki da magoya bayan kanar Gaddafi sun kai hare hare a garin, inda wuta ke ci gaba da ci, yayin da bakin hayaki ya tirnike sararin samaniya.

Wani mazaunin garin wanda bai son a ambaci sunansa, ya shaidawa BBC cewa sun kudiri aniyar cewa sai sun hambarad da gwamnatin kanar Gaddafi.

A waje daya kuma 'Yan tawayen a gabashin kasar na ci gaba da kara matsawa kusa da garin Sirte, yankin da magoya bayan kanar Gaddafi keda karfi, inda suka `kwace iko a Bin Jawad, wani `kauye mai nisan kilomita dari da hamsin daga garin na Sirte.