An nemi da rusa hukumar tsaron kasar Masar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga zanga a kasar Masar

Masu zanga zanga sunyi jerin gwano zuwa ofishin jami'an tsaro na farin kaya dake birnin Alkahira, inda suka nemi da rusa hukumar tsaron kasar

Rahotanni daga kasar Masar sun ce masu zanga zanga sunyi jerin gwano zuwa ofishin jami'an tsaro na farin kaya dake birnin Alkahira, inda suka nemi da rusa hukumar tsaron kasar.

A daren jiya ne dai masu zanga-zanga suka afka Hedkwatar Hukumar leken asirin kasar dake birnin Iskandriya,inda suka tilastawa rundinar sojan kasar karbe iko a ofishin.

Bukatar neman a rusa hukumar tsaron farin kayan dai na daya daga cikin manyan bukatun da 'yan adawa suka nemi ayi, tun bayan da suka tilastawa shugaba Hosni Mubarrak sauka daga karagar mulki.