Ana zargin kwasar ganima a Cote d'ivoire

Wasu na hannun daman mutumin da kasashen duniya suka amince da shi a matsayin shugaban kasar Cote D'Ivoire Alassane Ouattara, sun ce magoya bayan abokin hamayyarsa, Laurent Gbagbo sun shiga gidajensu don kwasar ganima a birnin Abidjan.

An bada rahoton cewa wasu gungun matasa da 'yan sanda ke ba kariya, sun loda kayayyakin ministoci da wasu kusoshin gwamnatin Mr Ouattara a cikin wasu manyan motoci, suka yi awon gaba da su.

A halin da ake ciki kuma, kungiya tsoffin 'yan tawaye ta New Forces ta ce ta kwace garin Toulepleu na Yammacin kasar daga hannun dakarun dake biyayya ga Mr Gbagbo.