Hare-hare kan juna na ci gaba a Libya

Barin wuta a Libya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana ci gaba da gumurzu a wasu yankunan Libya.

Ana cigaba da gwabza mummunan fada a Gabashi da Yammacin kasar Libya yayinda sojojin da ke biyayya ga Kanar Gaddafi ke yunkurin kwato yankunan dake hannun 'yan tawaye.

Dakarun 'yan tawaye sun ce sojojin gwamnati, wadanda helikoftocin yaki ke ba kariya, sun kai hari a kan garin Bin Jawad, wanda ya fada hannun 'yan tawaye a jiya.

Can a Yammacin kasar kuma, tankokin yaki suna kai hari a kan birnin Misrata, wanda shi ma ke hannun 'yan tawaye. A birnin Tripoli kuwa, karar harbin bindigogi aka ji yau da asubahi, amma gwamnati ta ce magoya bayan Kanar Gaddafi ne ke murnar irin nasarorin da suke samu a wasu yankuna.