Gaddafi ya gargadi kasashen Yamma

Libya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun 'yan adawa a birnin Zawiya

Kanar Gaddafi ya gargadi kasashen yammacin Turai cewa, kasashensu za su cika da 'yan gudun hijira idan basu taimakawa Libya ba a yakin da yace tana yi da kungiyar al-Qaeda.

A hirar da yayi da wata jaridar Faransanci, Kanar Gaddafi ya kuma ce, rashin zaman lafiya a Libya zai iya sawa kasar ta fada hannun Osama bin Laden.

Tun farko dai masu adawa da Kanar Gaddafi sun ayyana kafa tasu gwamnatin da suka ce, ita ce kadai halastacciyar hukuma dake wakiltar mutanen kasar Libya.

Kanar Gaddafi ya bayyana matukar damuwa kan yadda kasashen duniya suka juya masa baya, a lokacin da yace yafi kowanne cancanta su taimaka masa kan 'yan ta'adda.

Yace na yi mamaki, cewa babu wanda ya fahimci cewa wannan fada ne muke yi da 'yan ta'adda.

Yace a baya Libya ta yi aiki tare da kasashen Yamma -- amma me yasa yanzu za a kyale ta ita kadai ba tare da tallafi ba.

Gaddafi ya yi gargadin cewa idan masu boren sukai nasara, to yankin tekun Mediterranean zai fada hannun masu jihadin Islama, inda mutanen Osama Ben Laden za su mamaye yankin baki daya.