Ana harbe-harbe a birnin Tripoli

Libya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun 'yan tawayen Libya

An wayi gari da jin kararrakin bindiga da makaman atilare ba kakkautawa a sassa da dama na Tripoli babban birnin Libya.

Wakilin BBC da ke birnin na Tripoli yace, wannan ita ce musayar wuta mafi girma a birnin.

Sai dai mai magana da yawun gwamnati ya ce dakarun kanar Gaddafi ne ke harba bindigogi saboda murnar nasarar da suka samu a kan 'yan tawaye, sai dai BBC ba ta kai ga tabbatar da kalaman na sa ba.

Kuma a yanzu birnin da ake ganin na da nisa da rikicin da ake yi, shi ma na da hadarin gaske.

Gidan talaninjin na kasar ya nuna magoya bayan Gaddafi na taruwa a wani dandali a birnin na Tripoli.

A yanzu gwamnati ta ce dakarunta sun kwace garuruwan Zawiya da Misrata da kuma garin Tabruk wanda ke kusa da garin Benghazi daga hannun 'yan tawaye, sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan.

Kanar Gaddafi dai na sane da mahimmancin birnin na Tripoli a gare shi, kuma yana hannunsa dari-bisa-dari.

Amma a 'yan kwanakin nan, duk da yunkurin gwamnati na yin duk mai yiwuwa wajen kawar da 'yan tawaye, ana samun fadi tashin 'yan adawa a birnin.