An bada belin Senata Lado Dan Marke a Katsina

Senata Lado Dan Marke
Image caption Senata Lado Dan Marke

A birnin Katsina na Najeriya, kotu ta bada belin dan takarar gwamna a jihar na jam'iyyar hamayya ta CPC, Alhaji Yakubu Lado Dan Marke.

Ranar Jumma'a ne dai 'yan sanda suka kama Alhaji Yakubu Lado Dan Marken bisa tuhumar hannu a wani zargin eho da kuma jifan tawagar gwamnan jihar ta Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema.

Ita dai jam'iyyar CPC ta yi ta fitowa tana musanta zargin tana cewa, dalilan siyasa ne suka sa aka kama dan takarar nata. A yanzu an tsayar da nan da makonni biyu masu zuwa domin ci gaba da sauraron wannan kara.