Musulmi sun yi zanga-zanga a New York

Musulmi masu zanga-zanga a New York
Image caption Musulmi masu zanga-zanga a New York

Daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a birnin New York don nuna rashin amincewa da wani zaman jin bahasi da Majalisar Dokokin Amurka za ta gudanar a wannan makon.

Duk da ruwan saman da aka sheka, masu zanga-zangar sun yi jerin gwano a titunan birnin na New York dauke da allunan da ke cewa 'Yau ni ma Musulmi ne'.

Daruruwan Musulmi ne da ma wadanda ba Musulmi ba suka fita don nuna rashin amicewarsu da zaman jin bahasin.

Wani dan jam'iyyar Republican, kuma shugaban Kwamitin Tsaron Kasa na Majalisar, Peter King, ya gayyaci mutane da dama don su bayar da shaida a kan yadda tsattsauran ra'ayin addini ke yaduwa a tsakanin al'ummar Musulmin Amurka.

Mista King, wanda ke wakiltar New York a Majalisar, yana kuma son a binciki irin matakan da shugabannin Musulmi ke dauka don fuskantar barazanar tsattsauran ra'ayi a tsakanin mabiyansu.

A cewarsa wadansu shugabannin Musulmin ba sa bayar da gudummawar da ta kamata ga jami'an 'yansanda da na hukumar tsaro ta FBI a binciken da suke yi na ayyukan ta'ddanci a kasar.

To amma masu zanga-zangar, da ma wadansu mutanen, na nuna fargabar cewa zaman jin bahasin ka iya rura wutar kin jinin Musulunci a Amurka.

A baya dai kalaman Mista King sun harzuka jama'a, kuma mutane da dama sun yi imanin wadanda ya gayyata su bayar da shaida ba sa wakilatar ra'ayin akasarin Musulmin kasar.