Shugaban Nijar ya sa hannu a kundin hada kan Jumhuriya

Wata rumfar zabe a Jumhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata rumfar zabe a Jumhuriyar Nijar

A jamhuriyar nijar yau ne wakilan rundunonin sojan kasar da wakilan jam’iyun siyasa ,da na kungiyoyin kwadago da kungiyoyin addinai da kungiyar sarakunan gargajiya da ma kungiyoyin yan jarida suka rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar cewa za su kiyaye da duk wani abin da zai mayar da hannun agogo baya a kasar nan gaba.

Wani biki ne na musamman gwamnatin mulkin sojan kasar ta shirya a kan haka,kuma rediyo da talbijin na gwamnatin suka gabatar kai tsaye.

A zaman da majalisar tuntubar juna ta yi a baya bayan nan ne ta yi na’am da daftarin kundin wanda ake jin zai taimaka wajen wanzar da zama lafiya da demokaradiya mai dorewa a kasar, wadda ta yi fama da rigingimu na siyasa a shekarun baya.

A ranar 12 ga wannan watan ne dai ake gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu tsakanin Alhaji Mahamadu Isufu na PNDS- Tarayya da Alhaji Seyni Umaru na MNSD- Nasara a dangane da alkawarin da hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar suka yi na maido da kasar bisa tafarkin Demokaradiya.