Ana tunanin daukar matakin soja a Libya.

Wata mata rike da bindiga a Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikicin Libya na kara kamari.

Shugaba Barack Obama ya ce Amurka da kawayen kasar a kungiyar tsaro NATO, har yanzu suna tunanin daukar matakin soji a kan halin da ake ciki a Libya, inda ya ce mutanen kasar suna fuskantar amfani da karfin da ba za a amince da shi ba.

Sai dai Russia ta ce ba ta goyon tsoma baki da karfi a kasar.

Shi kuma Babban Magatakardan NATOn ya ce suna nan suna shiri cikin hikima.

Shi ma Firaministan Biritaniya ya amsa cewa suna aiki tare da sauran kawaye a kan irin kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ake jiya don samun izni.